ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Siriya ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake gabatar da jawabi a gaban sabuwar majalisar dokokin kasar wacce ta fara aikinta a ranar Litinin da ta gabata a birnin Damascus babban birnin kasar a jiya Laraba.
Shugaban ya kara da cewa hare-haren da sojojin HKI suke kaiwa kan wasu wurare a cikin kasar Siriya da kuma takunkuman da Amurka ta dorawa kasar da kuma kawayenta duk suna nufin karfafa kungiyoyin yan ta’adda a yankin ne.
Wannan dai ita ce majalisar dokoki ta uku a kasar Siriya tun bayan samun nasarar kwace mafi yawan kasar daga hannun yan ta’adda.
342/